Yaƙi: Shugaban Ukraine Ya Nemi Ɗaukin Najeriya da Cote d’Ivoire

135

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya roƙi Najeriya da Côte d’Ivoire da sauran ƙasashen Afirka da su kawo masa tallafi a yaƙin da ƙasarsa take yi da Russia.

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Alhamis a yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar ta Intanet.

Shugaba Zelensky ya ce ya tattauna da shugabannin Afirka da dama da suka haɗa da na Najeriya da Côte d’Ivoire a ƙoƙarinsa na ƙulla alaƙar tattalin arziƙi da su.

Ya ƙara da cewa zuba jarin da Ukraine za ta yi a Afirka zai samar da ayyukan tattalin arziƙi, musayar al’adun zamantakewa da abinci ga ƙasarsa.

“Na yi magana da shugabannin Afirka da yawa a Najeriya da Côte d’Ivoire. Na yi imani dole mu kafa kyakkyawar alaƙa duk da yaƙin da muke ciki. Zai yi min wahala, amma ina son ƙawancen ƙasashen Afirka su ba mu dama mu samar musu da abinci.

“Muna son a yi musayar al’adun zamantakewa. Ina son ‘yan Ukraine su zuba jari a Afirka, su ma ‘yan Afrika su zuba jari a Ukraine. Na san yadda ake yi wa ƙasarmu kallon raini, na san kuma ana yi wa ƙasashen Afirka kallon raini, ina so mu sauya haka”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan