Alfanun Da Za A Samu Idan Aka Tsige Buhari— Abba Hikima

210

Fitaccen lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Barista Abba Hikima, ya lissafo wasu abubuwa da ya bayyana a matsayin alfanu da za a samu idan ‘yan majalisar Najeriya suka tsige Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

Barista Hikima ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma’a.

Ya ce:


“Cire Buhari daga mulki zai yi matukar amfani kamar haka:

  1. “Zai zama misali da jan kunne ga shugabannin da za su zo bayan shi.
  2. “Zai nuna riƙar dimukraɗiyyar Najeriya.
  3. “Zai ƙara ƙarfafar ‘yan majalisa wajen aiki da shata layi tsakaninsu da ɓangaren zartarwa. Domin yanzu haka a tarihin Najeriya, ba wai cire shugaban ƙasa ba, hatta ‘vetoing’ (fin ƙarfin sa) sa akan doka ko bill (ƙudiri) sau uku aka taɓa yi tun 1963. Ka iya cewa ‘yan amshin shata ne.
  4. “Zai sa ‘yan majalisa su haɗa kansu akan ci gaban Najeriya ba goyon bayan jam’iyyunsu na siyasa ba.
  5. “A sauran watanni 8 da za su yi saura, za a iya samun canji ba kaɗan ba. Duk da VP (Mataimakin Shugaban Ƙasa) nada nashi damuwar, amma dukkan mu mun yarda cewa sadda aka miƙa masa mulki ya taka rawar gani. Har saida dala ta sauko.

“Da sauran alfanu da dama. Saboda haka gara ya tafi. Dare ɗaya Allah kan yi Bature”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan