Halin Da Najeriya Ke Ciki Yanzu Ya Fi Na 2015 Muni— Halifa Sanusi II

222

Tsohon Sarkin Kano kuma Halifan Tijjaniyya a Najeriya, Muhammad Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da halin da Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Ya ce halin da Najeriya ke ciki yanzu ya fi na 2015 muni lokacin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya karɓi mulki daga tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan.

Halifa Sanusi II ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Legas a yayin wani taron kan shugabanci da gidauniyar Akinjide Adeosun Foundation, AAF, ta shirya.

“Wannan ita kadai ce ƙasa mai arziƙin man fetur da take kuka a yanzu duk da farashin man fetur ya yi sama sakamakon yaƙin Russia/Ukraine. Gaba ɗaya kuɗaɗen shigarmu sun gaza biyan bashin da ake bin mu. Kuma idan ma ba wanda ya san cewa muna cikin komaɗar tattalin arziƙi, to muna ciki.

“Muna cikin wani ƙaton kwazzabo a 2015. Daga 2015 zuwa yanzu, mun ci gaba da faɗawa cikin kwazzabo mafi zurfi.

“Mun yi tunanin muna da babbar matsala a 2015. 2015 ba komai ba ce idan aka kwatanta da abin da zai faru a 2023. Muna da ta’addanci, muna da fashin daji, muna da hauhawar farashi, muna da rashin tabbas a kasuwar canji, kuma abu mafi muni shi ne shugabanni suna tunanin za mu gode musu idan suka bar ofis, suna tunanin za mu yaba musu. Babu wani canji”, in ji Halifa Sanusi II.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan