Jaruma Zahrah Diamond ta dawo ruwa tsundum!

241

ARUMAR Kannywood mai tasowa, Zarah Muhammad (Zarah Diamond), wadda ta yi aure a asirce a cikin 2021, ta dawo ruwa, domin kuwa alamu sun nuna auren ta ya mutu.

Tun daga irin hotunan da ta ke ɗorawa a Instagram da kuma bidiyon da ta ke yi a TikTok ya sa mutane su ka fara tunanin babu auren.

A ranar 4 ga Yuni, 2022 jarumar ta ɗora wani bidiyo inda ta nuna su na aikin wani fim mai dogon zango mai suna ‘Amaryar Shekara’, wanda darakta Ibrahim Bala ke bada umarni, inda ita kuma ta fito a matsayin likita mai suna Dakta Ameera.

Jarumar ta ɗora hotuna aƙalla 11 da bidiyo ɗaya na wannan aikin da su ke yi. A lokacin ne mutane su ka tabbatar da auren ta ya mutu.

Haka kuma kwanan nan Zarah ta shiga Instagram ta rubuta cewa: “Ni ba aure zan ba, aiki ne na waƙa da fim wanda su ne sana’a ta, pls.”

Dalilin da ya sa jarumar ta yi wannan rubutu kuwa, an ga wasu hotuna ne da ta ɗauka tare da mawaƙi Abba Harara, wanda su ka yi kama da hotunan kafin aure (pre-wedding pictures), sai mutane su ke ganin kamar aure ta sake yi.

Wakilin mu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin jarumar kan wannan al’amari, amma hakan bai yiwu ba, don har tsawon lokaci wayar ta ba ta shiga idan aka kira, da alama ta canza layin waya.

Idan za a iya tunawa, Labarai24 ta ba ku labarin yadda jarumar da kan ta ta ba furodusoshi da daraktoci haƙuri a lokacin auren nata a wancan lokacin, ta ce: “Salam masoya na, ‘producers’ ɗi na, ‘directors’ da abokan aiki na, waɗanda na gama da kuma waɗanda ban gama ba, ina mai ba su haƙuri, saboda yanayin zaɓin da Allah ke yi wa dukkanin bayin sa, to ya min zaɓi mafi alkairi a gare ni, saboda haka ba ni da baki ko ‘yancin ƙarasa muku ayyukan ku.

“Fatan za ku fahimce ni? Allah ya ba ku haƙuri ya kuma musanya muku da alkairi.”

Haka kuma ta yi kira ga mamallakan shafukan mabiyan ta da su cire hotunan ta da bidiyoyin ta daga shafukan, domin fa ita ta yi bankwana da harkar fim.

A saƙon kiran Zahra Diamond ta ce, “Don Allah masu ‘fans page’ ɗi na, ku yi haƙuri ku dubi girman Allah ku cire hotuna ɗi na da kuma bidiyo-bidiyo ɗi na, kuma ku canza suna na. Na gode.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan