Wani Ɗalibi A Kwara Ya Kashe Kansa Sakamakon Faɗuwa Jarrabawa

105

Wani ɗalibi mai suna Adegoke Adeyemi, ɗan shekara 17 dake makarantar Offa Grammar School, a ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara, ya kashe kansa sakamakon faɗuwa jarrabawar zuwa ajin gaba.

Adegoke, wanda aka same shi a rataye akan wata bishiya, ya yanke shawarar kashe kansa ne saboda ya gaza zuwa SS 2.

Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kwara, SP Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar wannan al’amari ranar Laraba.

Ya ce: “Ɗalibin, Adegoke Adeyemi, ɗan shekara 17, wanda yake a Offa Grammar School, an yi imanin ya rataye kansa sakamakon faɗuwa jarrabawar zuwa ajin gaba da ya yi daga SSS 1 zuwa SSS 2, abin da ya sa dole sai ya maimaita aji.

“Jami’in ‘Yan Sanda na Offa, ya samu bayani ranar 2 ga Agusta, 2022 da misalin ƙarfe 3:34 cewa an samu wata gawa akan wata bishiya a Ariya Garden Hotel, Offa. Nan da nan sai aka tura tawagar ‘yan sanda zuwa wajen”, in ji Mista Ajayi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan