Zan koma harkokin kwangila idan na kammala mulki — Gwamna El-Rufa’i

295

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya bayyana cewa idan ya kammala wa’adin mulkin jihar ba zai karɓi wani muƙami daga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba, inda ya ce sai dai ya zama ɗan kwangila.

El-rufai ya bayyana haka ne a cikin wani shiri da ake gabatarwa a sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) a jiya Juma’a, ya ce shi yanzu ya wuce ya karɓi wani muƙami, inda ya ƙara da cewa sai dai a barwa wasu su yi.

A cewar sa, tuni ya faɗa wa Tinubu cewa idan ya ci zaɓe sai dai ya riƙa bashi kwangila, ya ƙara da cewa dama ya san Tinubu kuma ya san wasu ministocin da zai naɗa.

Ya ce bai kamata a riƙa nacin riƙe muƙami ba, inda ya nuna cewa kamata ya yi a riƙa bar wa ƴan baya su ma su ɗana.

“Na yi minista ina da shekara 43. Yanzu ina da shekara 63, kawai sai in zo in karɓi muƙamin minista? Ina da ƴaƴa da ƙanne da ƴan uwa, sai in bar musu suma su ɗana.

“Dama na taɓa rubuta littafi kuma na samu kuɗi, saboda haka idan na gama mulki zan sake rubuta wani littafin domin in samu kuɗin fansho da kuma kuɗin makarantar yara.

“Sai kawai na zama ɗan kwangila yadda ake yi, tuni ma na faɗa wa Asiwaju haka. Dama Asiwaju ya san ni kuma na san mataimakin shugaban kasa kuma zan san da yawa daga cikin ministocin da zai naɗa,” in ji El-Rufa’i

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan