2023: Mutum huɗu ne kacal su ka rage a jam’iyyar APC

  176

  Lokacin da aka kafa jam’iyyar APC a shekarar 2013, duk mutanen Najeriya suna cikinta. Kadan ne basa tare da ita. A shekarar 2015 da aka yi zabe, kwai da kwarkwata aka hadu aka zabi jam’iyyar APC. A wannan lokacin APC jam’iyyar Najeriya ce ta mutanen Najeriya don ‘yan Najeriya. Shekara bakwai da doriya, yanzu jam’iyyar APC ta koma ta mutum bakwai.

  Ga su zan jero su ;

  Na Farko:
  Shugaban kasa Muhammad Buhari da matarsa da ‘yan uwanta da ‘ya’yansa da jikokinsa da ministoci da duk wadanda aka nada a mukami a tarayya ko a kasar waje.

  Na Biyu
  Sanata Bola Ahmed Tinubu dan takarar shugabancin Najeriya da mataimakinsa, Kashim Shettima da gwamnonin da suke neman tazarce a zaben 2023 a tutar APC da ‘yan takarar gwamnoni a APC da ‘yan takarar majalisar tarayya da ta dattijai da jiha da duk GT to to go suke tare da su a nadi na mukami a duk matakai.

  Na Uku
  Shugabannin jam’iyyar APC a matakin kasa da jiha da shiyya da kananan hukumomi da mazabunsu da caftoci, wadanda suna saka rai su kara sa wa’adin zamansu a kujerun da kuma wadanda suke jiran karbar kayan aikin zabe na 2023. In sun karba su kama gabansu.

  Na Hudu;
  Manyan ƴan kasuwa masu jari da manoma da ‘yan kwangila da masu masana’antu da kamfanoni da aka buda musu hanyoyin samun kudi da kara musu jari, da manyan ma’aikatan gwamnati masu fada aji da ludayin su yake kan dawo.

  Wadannan nau’in mutane hudu sune kadai suke juya lamuran yau a fagage a kasar nan. Sauran jama’a kuma sai LAHAULA. Sauran jama’a KO OHO !!! Sauran jama’a suna WAHALA.

  Bello Muhammad Sharada ya rubuto daga Kano – Najeriya

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan