Burkina Faso Ta Nemi Shawarar Najeriya Kan Yaƙi Da Ta’addanci

115

Gwamnatin ƙasar Burkina Faso ta nemi shawarar Najeriya kan yadda za ta yaƙi ta’addanci a ƙasar.

Shugaban Jami’an Tsaro na Burkina Faso, David Kadre ne ya nemi shawarar a Abuja lokacin da ya ziyarci takwaransa na Najeriya, Lucky Irabor.

Ya ce ya zo Najeriya ne don ya halarci bikin kammala karatu na ɗalibai 30 da Makarantar Nazarin Tsaro ta ƙasa ta yi.

“Na zo don mu tattauna batun ta’addanci da tada ƙayar baya a ƙasashenmu don neman shawararku da gogewarku tun da Najeriya tana kan yaƙin wannan abu a halin yanzu”, in ji Mista Kadre.

Mista Kadre ya ce akwai buƙatar a samu haɗin kai tsakanin dakarun Najeriya da na Burkina Faso don kawo ƙarshen ta’addanci da tada ƙayar baya a ƙasashen biyu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan