‘Yan Taliban Sun Lakaɗa Wa Mata Masu Zanga-Zanga Duka

180

Mayaƙan Taliban sun yi harbi a iska tare da dukan wasu mata da suka fito suna zanga-zanga a babban birnin ƙasar, Kabul.

Matan sun fito zanga-zangar ne don nuna damuwarsu bisa abin da suke kira danne haƙƙinsu da gwamnatin Afghanistan tun lokacin da suka dawo kan mulki kimanin shekara ɗaya da ta gabata.

A ranar 15 ga Agusta, 2021 ne ‘yan Taliban suka dawo mulkin Afghanistan bayan da Amurka ta shafe shekara 20 tana mulki a ƙasar.

Matan su kusan 40 sun yi dandazo a ofishin Ma’aikatar Ilimi ta Afghanistan suna rera waƙoƙin zanga-zanga daban-daban.

‘Yan Taliban sun daki wasu matan da suka ɓoye a cikin wasu shaguna a yayin zanga-zangar.

Masu zanga-zangar sun riƙe wani ƙyalle dake ɗauke da rubutun: “15 ga Agusta baƙar rana ce”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan