Za mu iya kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin wata 6 – Kungiyar Fulani

185

Kungiyar Fulani ta ƙasa da ƙasa, mai suna Tabital Pulaaku International a Najeriya ta ce za ta shawo kan matsalolin tsaro cikin wata shida idan ta samu haɗin kan gwamnatin ƙasar.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a wurin wani taro na masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja a jiya Lahadi.

Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Isa Yuguda, shi ne zaɓabɓen shugaban ƙungiyar kuma ya shaida wa BBC Hausa irin abubuwan da kungiyar za ta saka a gaba don gano bakin zaren matsalar tsaron.

“Lallai za mu ƙirƙiro hanyoyin da waɗannan matasa za su fito daga daji su rungumi wannan al’ada ta fulaku wato jin kunya da girmama mutane,” a cewar Isa Yuguda.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan