Ana zargin fitattun jaruman Kannywood 2 da cinye tallafin A.A. Zaura

302

WATA sabuwar dambarwa ta na neman ɓullowa a masana’antar finafinai ta Kannywood a sakamakon zargin da ake yi wa wasu fitattun jarumai na handame kayan tallafin da wani babban ɗan siyasa ya ba ‘yan fim.

Waɗanda ake zargin dai su ne T.Y. Shaban da Shariff Aminu Ahlan, waɗanda su ne shugabannin wata ƙungiya mai suna ‘Kannywood Celebrity Forum’ (KCF4AAZAURA) wadda aka kafa domin ciyar da manufofin fitaccen ɗan siyasar nan da ya yi takarar gwamnan Kano, Abdukareem Abdulsalam Zaura, wanda ake yi wa laƙabi da A.A. Zaura, gaba, musamman a masana’antar. Daga baya ya dawo ya na takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.

Ƙungiyar, wadda aka kafa kusan shekara ɗaya da ta gabata, ta ƙunshi jarumai da mawaƙa da sauran su, waɗanda su ka haɗe waje guda su na yin aiki tare, har ana ganib ba a taɓa samun haɗuwar ‘yan fim sun yi haka ba wajen tafiya wajen ɗaya.

Domin su ƙara ƙarfin tafiyar tasu, watanni bakwai da su ka gabata sun yi wani taro na musamman inda suka gayyato A.A. Zaura ɗin su ka karrama shi da lambar yabo mai girma tare da nuna masa su ne masoyan sa na haƙiƙa kuma sun shirya tsaf domin yaɗa kyawawan manufofin sa ga jama’ar jihar.

Ganin yadda su ka yi masa wannan karramawar, a nasa ɓangaren sai ya nuna jin daɗin sa sannan ya yi wa ‘yan ƙungiyar alƙawarin zai ba da wata gudunmawa ga masana’antar fim wadda ya kira da tallafin da ba a taɓa yin kamar sa ba.

Wannan ta sa ‘yan fim su ka shiga tsalle su na murna. A zaton su, gudunmawar za ta zo yau ko gobe ko jibi. Kuma abin ka da ‘yan fim, wasu har sun fara shirya abin da za su yi da kayan nasu idan ya zo gare su.

Sai dai yanzu rabin shekara kayan bai samu ba. Wasu sun fara ƙorafin yadda aka yi kayan bai samu ba, duk kuwa da yake shi A.A. Zaura ɗin ya ci gaba da raba kayan tallafi da bayar da gudunmuwa ga ƙungiyoyi da kuma ɗaiɗaikun mutane.

Ko a ranar Talata da ta gabata an gan shi a fadar gwamnatin Jihar Kano ya na raba kekunan ɗinki sama da 10,000 ga ƙungiyar teloli ta jihar.Wannan ya ƙara fito da ƙorafin da ‘yan fim ke yi inda su ke jefa ayar tambaya ga nasu shugabannin, su na cewa ko dai an ba su Shaban da Ahlan kayayyakin sun rabe a tsakanin su ba tare da sun gayyato ɗan siyasar zuwa bikin rabon ba kamar yadda sauran ƙungiyoyi su ke yi.

Wannan ya ƙara fito da ƙorafin ‘yan fim ke yi inda su ke jefa ayar tambaya ga nasu shugabannin, su na cewa ko dai an ba su Shaban da Ahlan kayayyakin sun rabe a tsakanin su ba tare da sun gayyato ɗan siyasar zuwa bikin rabon ba kamar yadda sauran ƙungiyoyi su ke yi.

Wasu kuma na zargin ko sun bi ta bayan gida ne sun karve kuɗin a maimakon kayan da za a raba wa jama’a su ka yi gaban kan su. Don haka ne ma wasu su ka yi yunƙurin ƙwatar wa kan su haƙƙin su a wajen shugabannin nasu ko dai su fito masu da kayan da aka ba su ko kuma su yi masu bayanin da zai gamsar da su.

Har zuwa yanzu dai Shaban da Ahlan ba su ce komai ba a kan wannan dambarwa da ta taso.

To sai dai Labarai24 tayi ƙoƙarin samun T.Y Shaban amma haƙan nata ya ci tura.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan