Na Ƙi Yin Aiki A Jami’ar Dubai Saboda Kishin Najeriya— Malami A Jami’ar Bayero, Kano

139

Mohammed Shaibu Atabo, wani malami a Jami’ar Bayero, Kano, ya ce ya yi watsi da wani aiki da ya samu a Jami’ar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAEU, Dubai, saboda kishin Najeriya.

Malam Atabo ya ce ya samu aikin ne tun kafin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta fara yajin aiki.

Idan dai za a iya tunawa, ASUU ta fara yajin aikin sai-baba-ta-gani ne ranar 14 ga Fabrairu, 2022.

Malam Atabo ya ce yau Laraba shekara ɗaya kenan da ya yi watsi da aikin da ya samu a waccan jami’a.

“Wannan mataki ne mai tsauri da na ɗauka saboda kishin ƙasata. Na zaɓi in tsaya in yi aiki a BUK maimakon tafiya ƙasar waje. Na sha suka daga iyalina da abokai sakamakon ɗaukar wannan mataki”, in ji shi.

Ya ce bayan wata shida da fara wannan yajin aiki, maimakon gwamnatin Najeriya ta warware matsalar sai ma ta yi wa ƙungiyar barazanar ƙin biyan ta albashi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan