Jami’an Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Najeriya, NCS, da aka fi sani da kwastam, sun harbi wani mamba na Ƙungiyar Direbobi ta Ƙasa, NURTW, a ƙaramar hukumar Garki dake jihar Jigawa.
Mai Magana da Yawun Hukumar tsaro ta NSCDC, CSC Adamu Shehu ne ya bayyana haka ranar Alhamis a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce ana zargin bulet ne ya samu mutumin lokacin da jami’an kwastam ɗin suke bin wani mutum da suke sa ran ɗan simoga ne da gudu.
A cewar Adamu, mutumin mai suna Abdurrahman Mohammed yana goge motarsa ne a Garki lokacin da ya hango motar jami’an kwastam tana tahowa da gudu.
Rahotanni suka ce nan da nan sai jami’an hana fasa ƙwaurin suka tsaya, ɗaya daga cikinsu ya harbe mutumin duk da roƙon su da wani soja ya yi.
Adamu ya ce nan da nan sai jami’an suka bar wajen.
Sanarwar ta ce mutumin bai mutu ba saboda bulet ɗin ya ɗan taɓa cikinsa ne.
Tuni dai mutumin ya samu kulawar likitoci a Babban Asibitin Garki.