2023: Yakubu Dogara ya buƙaci kiristocin Najeriya da su ƙauracewa zaɓen jami’yyar APC

110

Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya, Yakubu Dogara ya yi kira ga daukacin al’ummar kiristocin Najeriya da su ƙauracewa zaɓen jam’iyyar APC a babban zaɓen shekarar 2023, saboda hakan ɓata lokaci ne da kuma asarar ƙuri’a.

Yakubu Dogara ya bayyana hakan ne a yau Talata a wajen taron gamayyar ƙungiyoyin kiristocin Najeriya da ya gudana a birnin tarayya Abuja.

Ya ce ya kamata ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya ɗauki mataimaki daga cikin kiristocin arewacin Najeriya, amma sai ya ɗauki tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

Mista Dogara ya ce Tinubu ba iya ƙin ɗaukar shawarar ɗaukar mataimaki musulmi ya yi ba kawai da ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta ba shi watsi ya yi da shawarar gaba ɗaya. Ya ce a dan haka dole ne a farkar da dukkanin mambobin coci – coci halin da ake ciki tare da yin watsi da matakin da jam’iyyar APC mai mulki ta ɗauka.

Hakazalika Yakubu Dogara ya ce yadda wasu malaman addinin Islama da shugabannin Musulmi suka yi tir da matakin da jam’iyyar APC ta ɗauka na baiwa Musulmi da Musulmi tikiti ya tabbatar da cewa matakin da kiristocin za su dauka yana bisa turba.

A lokacin taron majalisar kiristocin ta Najeriya Yakubu Dogara ya ce ” Ina kira ga kiristocin Najeriya kaf ɗin su ka da su barnata ƙuri’un su wajen zaɓen jam’iyyar APC da suka tsaida Muslim-Muslim, domin Najeriya ba ta musulmai ba ce kaɗai. Lallai Kiristoci su ƙauracewa jami’yyar APC domin addinin mu ya yi hani da ɓarnata abu”

“Mun gargaɗi APC ka da su yi wannan ganganci na Muslim-Muslim amma suka yi mana kunnen uwar shegu suka tsaida musulmai biyu. Muna tabbatar muku mu kiristocin kasar nan za mu nuna musu ba su isa ba. Saboda haka kada wani kirista ya zaɓi APC domin barnar kuri’an sa kawai zai yi.” In ji Yakubu Dogara

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan