An Gurfanar Da Mutum 3 A Kotu Bisa Zargin Su Da Ɓata Sunan ‘Yar Sani Danja

85

Wata Kotun Majistire dake Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan, ta ba da umarnin a garƙame Jabir Muhammad, Abubakar Sunusi da wani da har yanzu ba a san inda yake ba a gidan gyaran hali bisa zargin su da buɗe shafuka a Facebook, Istagram, YouTube da Twitter da sunan Khadijatul Iman Sani Danja, ɗiya ga fitaccen jarumi a Kannywood, Sani Musa Danja.

Kotun na kuma zargin mutanen uku da wallafa hotunan da ba su dace ba da kuma damfarar mutane da shafukan da suka buɗe— laifukan da suka saɓa da sashi na 97, 324, 393 da 392 na dokar penal code.

Sai dai waɗanda ake zargin sun musanta zarge-zargen, sakamakon haka ne lauyansu ya roƙi kotun da ta ba da su beli.

Sai kotun ta ba da umarnin a gaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa 27 ga Satumba, 2022, ranar da za ta duba yiwuwar ba da belin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan