Hotunan Kammala Karatun Matar Yusuf Buhari Sun Harziƙa ‘Yan Najeriya

94

A ranar Talata ne Uwargidan Shugaban Najeriya, A’isha Buhari, ta wallafa hotunan kammala karatun matar Yusuf Buhari, wato Zahra Nasir Bayero.

A’isha Buhari ta wallafa hotunan ne a shafinta na Facebook inda ta taya surukar tata murna.

Zahra ta kammala digirin farko ne da Sakamako Mafi Kyau wato First Class a Jami’ar Surrey, Birtaniya.

Sai dai jim kaɗan da wallafa hotunan da A’isha Buhari ta yi ne sai ‘yan Najeriya suka fara mayar mata zafafan martani duba da yadda Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya, ASUU, ke ci gaba da yajin aiki, amma a daidai lokacin ita kuma take ɗora hotunan kammala karatun surukarta a ƙasar waje.

Ga wasu daga cikin irin martani da Labarai24 ta tattaro muku.

Muhsin ya ce: “Kada ku yi mamaki idan wasu daga cikin ‘yan gidan Uwargidan Shugaban Ƙasa ba za su iya faɗar cikakkiyar ma’anar ASUU ba, ko kuma ba su san yajin aikin da suka shafe watanni suna yi ba. Ba mamaki wani daga cikin ‘yan gidan ne ya wallafa waɗancan hotuna na bikin kammala karatun surukar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Idan ba haka ba, ni na rasa me zan ce.

“Na taɓa faɗa a baya. A’isha Buhari ba jaruma ba ce. A kwanakin baya ma ta yi ta kwarmato ne saboda wasu sun yi wa buƙatarta cikas. Ƙorafe-ƙorafenta ba kawai suna nuna rashin iya Huɗɗa da Jama’a a Fadar Shugaban Ƙasa ba, amma suna nuna tsantsar buƙatar kai. Ba ta taɓa kare ko yin kwarmato game da buƙatun talaka ba. Za ku iya ganin haka yanzu ƙuru-ƙuru.

“Matasa, zaɓen 2023 saura ‘yan watanni. Don Allah ku yi zaɓe cikin hikima. Kar ku bar mutanen nan su ƙara yaudarar ku.

“Ina yi muku fatan alheri daga Naples, Italy”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan