Walƙiya Ta Kashe Aƙalla Mutum 21 A Indiya

42

Aƙalla mutane 21 ne suka rasu a jihar Bihar dake Gabashin Indiya sakamakon mamakon ruwan sama da walƙiya da aka shafe sa’o’i 24 ana yi.

Wani jami’in Hukumar Kiyaye Afkuwar Ibitila’i ta Indiya ya ce waɗanda suka rasu manoma ne da suke ayyuka a gonakinsu.

A cewarsa, an samu mace-macen ne a larduna 10 dake jihar.

Mutum huɗu sun mutu a Purnia da Araria, uku a lardin Supaul, mutum uku a Banka, Jamui da Nawada, sai mutum ɗaya a Begusarai, Sheikhpura, Saran da Saharsa, kamar yadda jami’in ya bayyana.

Babban Ministan Bihar, Nitish Kumar, ya sanar da cewa za a ba iyalan da suka rasa ‘ya’yansu a wannan ibitila’i Rupee (INR) 400,000 ( kimanin dalar Amurka $5,023).

Mista Kumar ya shawarci jama’a da su dinga zama cikin shiri a irin wannan yanayi.

“Dole mutane su bi ƙa’idoji da Hukumar Kare Afkuwar Ibitila’i ta fitar don kare kansu daga haɗarin walƙiya.

“Dole mutum ya zauna a gida a lokaci mai iska”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan