Ganduje Zai Mayar Da Gidan Marigayi Ɗan Masanin Kano Gidan Tarihi

116

Gwamnatin jihar Kano ta karɓe gidan marigayi Yusuf Maitama Sule Ɗan Masanin Kano.


Kwamishinan Watsa Labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ne ya bayyana haka ranar Laraba a Kano.

Ya ce gwamnatin Kano za ta mayar da gidan gidan tarihi kuma cibiyar nazarin dimokuraɗiyya.

A cewar kwamishinan, za sa wa cibiyar ‘Cibiyar Bunƙasa Dimokuraɗiyya da Kyakkyawan Shugabanci’.

Ya ce tuni an fara gini a gidan da da ake kira British Council Library a da dake kan Titin Fadar Masarautar Kano.

Kwamishinan ya ƙara da cewa za a kashe jimillar kuɗi da suka kai N N621, 604, 295.89, kuma za a yi aikin a mataki biyu.

Za a fara aikin da gina gidan tarihin, daga baya kuma a gina cibiyar, kamar yadda ya bayyana, yana mai ƙarawa da cewa aikin zai kiyaye al’adun da tarihin al’ummar Kano domin ‘yan gaba, tare da zama wajen bincike da yawon buɗe ido.

“Banda haka ma ana sa ran cibiyar za ta dinga bayar da horo, killace bayanai da zamanantar da su, haɗa kai da cibiyoyin ilimi da takwarorinta a ciki da wajen Kano don gudanar da bincike”, in ji shi.

Marigayi Yusuf Maitama Sule dai ya rasu ranar 2 ga Yuli, 2017 a Masar yana da shekara 87.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan