Mutum 5 Sun Nitse A Kogi A Abuja A Ƙoƙarin Guje Wa Masu Garkuwa

68

Wasu mutane biyar a Abuja da suka haɗa da maza huɗu da wata matar aure sun nitse a cikin wani kogi a ƙoƙarinsu na guje wa masu garkuwa da mutane.

Mutanen sun nitse a kogin ne a ƙauyen Chakumi dake mazaɓar Gurdi a ƙaramar hukumar Abaji ta Abujan.

Chakumi ya yi iyaka da wani ƙauye mai suna Daku dake kusa da Kogin Gurara a mazaɓar Dobi dake ƙaramar hukumar Gwagwalada ta birnin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Dagacin Chakumi, Mohammed Magaji, ya tabbatar wa da Daily Trust cewa al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar Laraba.

Mutanen suna aiki ne a gona lokacin da suka hango masu garkuwar.

Nan da nan sai suka garzaya don su hau kwalekwale don su tsere zuwa Daku, suna ƙoƙarin ƙetare Kogin Gurara sai kwalekwalen ya kife, kamar yadda Mohammed ya bayyana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan