Ba Buhari Ne Matsalar Najeriya Ba— Fasto

84

Wani malamin addinin Kirista ɗan Najeriya mazaunin Birtaniya mai suna Apostle Alfred Williams, ya ce bai kamata a dinga sukar Buhari ba game da matsalolin Najeriya.

Williams ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wa tashar Gidan Talabijin na Ƙasa, NTA ziyara a Abekuta, baban birnin jihar Ogun.

A cewarsa, tsarin Najeriya ne ya daƙile kyakkyawar manufar Buhari ga Najeriya.

Ya ce idan ba a gyara tsarin Najeriya ba zai iya kawo tazgaro ga duk wani shugaba da zai zo.

“Buhari ba shi ne matsalar Najeriya ba. Matsalar Najeriya ita ce tsarin. Idan kai ko ni, ko Pasto Adeboye, wanda duka muke girmamawa, ko Fasto Kumuyi za su zauna a Fadar Shugaban Najeriya, za su fusata.

“Saboda haka ba maganar wanda yake kan shugabanci ba ne, tsarin ne yake daƙile duk wata kyakkyawar manufa. Idan muka yi ta zargin Buhari, duk wanda ya je can indai tsarin yana nan yadda yake, shi ma zai gaza kamar Buharin”, in ji Fasto Williams.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan