Saudiyya Ta Cika Shekaru 90 Da Kafuwa

51

Saudiyya ta cika shekaru 90 da kafuwa a matsayin dunƙulalliyar ƙasa.

A ranar 23 ga Satumba, 1932 ne aka kafa ƙasar bayan da yankunan Nejd da Hijaz suka haɗe wuri guda.

A duk irin wannan rana akan shirya bukukuwa a Saudiyya da suka haɗa da rawa, waƙe-waƙe da sauran bukukuwan gargajiya a dukkan faɗin ƙasar, kamar yadda shafin Facebook mai suna 5 Minute History ya wallafa.

Bayan masarautun Nejd da Hijaz sun haɗe ne sai aka sanya wa ƙasar suna Masarautar Saudiyya, kuma Sarki Abdul’aziz ibn Saud shi ne Sarkin Saudiyya na farko.

Hussein bin Ali ne ya kafa Masarautar Hijaz lokacin da ya yi wa Daular Ottoman bore a lokacin Yaƙin Duniya Na 1 a 1916.

Sai dai masarautar ba ta yi ƙarko ba domin a 1924 ne Nejd ta kai mata hari inda ta mamaye ta.

Daga 1925 zuwa 1925, iyalan Saudi suka ci Hashimawa da yaƙi suka haɗe da Hejaz.

Su kuma masarautun Hejaz da Nejd an samar da su ne a 1926.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan