Sauya Sheƙar Shekarau: NNPP Ta Faɗa Cukumurɗa Irin Ta Siyasa

92

Jam’iyyar NNPP ta Rabi’u Musa Kwankwaso ta faɗa cikin wata cukumurɗa irin ta siyasa saboda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, INEC, ta ce har yanzu Malam Ibrahim Shekarau ne ɗan takarar NNPP duk da barin jam’iyyar da ya yi.

A ranar 29 ga Agusta ne Shekarau ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa PDP, yana mai ba da dalilin cewa ba a yi masa adalci ba.

Sai dai abin da ya ba mutane mamaki shi ne yadda har yanzu INEC ba ta cire sunan Shekarau ba a matsayin ɗan takarar sanata na NNPP a Kano ta Tsakiya.

Kwamishinan Ƙasa na INEC kuma Shugaban Kwamitin Watsa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Festus Okoye, ya ce sanarwar da Shekarau ya ba INEC cewa ya bar NNPP ta zo a ƙurarren lokaci, saboda haka zai ci gaba da zama ɗan takarar NNPP a Kano ta Tsakiya.

“Bisa jadawali da tsarin aikace-aikacenmu da muka fitar ranar 26 ga Fabrairu, 2022, 15 ga Yuli ita ce ranar ƙarshe da za a iya janye ko sauya sunayen ‘yan takara. Tsohon Gwamnan na Kano ya janye takararsa ne ranar 26 ga Agusta, 2022.

“Abin da wannan ke nufi shi ne zai ci gaba da zama ɗan takarar NNPP. Sunansa zai fito akan ƙuri’a ranar zaɓe a matsayin ɗan takarar NNPP a mazaɓarsa ta sanata”, in ji Mista Okoye

Sakataren Watsa Labarai na NNPP a Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya ce ba su yi mamakin yadda sunan Shekarau ya fito ba, yana mai cewa sun fara ƙoƙarin gyara matsalar.

Rogo ya ce bisa tsare-tsare da INEC ta fitar, dole NNPP ta bi wasu matakai kafin a sauya sunan na Shekarau.

Ya ce tun da Shekarau ya bar jam’iyyar ne bisa raɗin kansa, jam’iyyar ta gabatar da sabon zaɓen fidda gwani a cikin lokacin da sabuwar dokar zaɓe ta tanada.

“Dukkan abin da muka yi yana cikin lokacin da aka ƙayyade kuma muna nan muna bin matakai da suka dace. Saboda haka mun tattara dukkan bayanai kuma za mu kai al’amarin kotu. Kuma bayan mun duba gaskiya da hujjojinmu, muna ta tabbas cewa kotu za ta umarci INEC ta sake sunan ɗan takarar baya ta sa sabon da za mu bayar. Yanzu muna jira kotu ta sa lokacin sauraron ƙara ne”, in ji shi.

Sai dai mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya’u Sule, ya ce duk da jadawalin da INEC ta fitar, matsayar Shekarau ba tare sauya ba.

“Ka san ya rubuta wasiƙa zuwa INEC cewa ya janye takararsa. An nuna wa jama’a kwafin wasiƙar; wannan shi ne matsayinsa”, in Sule.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan