Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Umarci A Buɗe Dukkan Jami’o’inta

146

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umarci dukkan shugabannin jami’o’inta da su buɗe su don ba ɗalibai damar ci gaba da karatu.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Kuɗi da Asusu na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya, NUC, Sam Onazi, ya fitar ranar Litinin a Abuja a madadin Shugaban Hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed.

Sanarwar da aka tura wa shugabannin jami’o’i, jagororin jami’o’i da shugabannin hukumomin gudanarwa na jami’o’in gwamnatin tarayya ta yi kira a gare su da su buɗe jami’o’in.

“A tabbatar da cewa mambobin ASUU sun dawo aiki tare da fara darasi, su dawo da ayyukan jami’o’i na yau da kullum daban-daban”, in ji sanarwar.

Idan dai za a iya tunawa, Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta fara yajin aiki ne ranar 14 ga Fabrairu, 2022, da nufin tilasta wa gwamnatin tarayya biya mata buƙatunta.

An yi tattaunawa daban-daban tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya amma abu ya ci tura.

Sakamakon haka ne Gwamnatin Tarayya ta maka ASUU a kotu don ƙalubalantar yajin aikin.

A ranar 21 ga Satumba, 2022 ne Kotun Ma’aikata ta umarci ƙungiyar ta dawo bakin aiki, amma ta ɗaukaka ƙara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan