Ana Sa Rai ASUU Na Dab Da Janye Yajin Aiki

193

Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce yana sa ran yajin aikin da ƙungiyar ta shafe wata takwas tana yi zai zo ƙarshe nan da ‘yan kwanaki kaɗan.

Farfesa Osodeke ya bayyana haka ne ranar Litinin a lokacin wata tattaunawa da Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Shugaban ya yaba wa Majalisar Wakilan bisa yadda ta tsoma baki a cikin yajin aikin, inda ya yi fatan cewa yajin aikin na gaba ba zai ja lokaci ba.

“Ya kamata gaba ɗayanmu mu yi aiki tare don kawo ƙarshen wannan yajin aikin da muka fara don kowane ɗan Najeriya ya yi alfahari cewa muna da jami’o’i da za mu yi alfahari da su.

“Ina gode muku. Ina kuma miƙa godiyarmu ga Shugaban Ƙasa bisa yadda ya tsoma baki. Ina so in yi roƙo cewa a nan gaba kaɗan, ba za mu bar yajin aiki ya yi tsawo ba. Bai kamata yajin aiki ya wuce kwana biyu ba”, in ji Farfesa Osodeke.

Shugaban na ASUU ya nuna rashin jin daɗi bisa yadda Ministan Ilimi, Adamu Adamu da Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi, Chris Ngige, suka yi wasarairai da yajin aikin.

“Da a ce ministocin ƙwadago da na ilimi sun yi abin da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta yi, da ba mu kasance a inda muke ba a yau. Da ba za mu wuce mako biyu ko uku akan wannan yajin aiki ba. Duk duniya ana yajin aiki—Birtaniya, Amurka—amma ba sa bari ya yi tsawo”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan