Yadda Barkwanci Tsakanin Nasir Zango Da Musa Majiya Ke Ƙayatar Da Jama’a

220

Nasir Salisu Zango fitaccen ɗan jarida ne da yake aiki a Freedom Radio, Kano.

Zango ya yi suna ne sakamakon shirin In Da Ranka na Freedom Radio, Kano, da yake gabatarwa a ranakun Litinin zuwa Juma’a.

ASP Magaji Musa Majiya kuma jami’in ɗan sanda ne kuma tsohon Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano.

A lokacin da yake kan wannan muƙami, Majiya ya jajirce sosai wajen sanar da ire-iren kame-kamen masu laifi da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano take yi.

Barkwancin da waɗannan mutanen biyu suke yi a kafar sada zumunta ta Facebook yana ƙawatar da mabiyansu matuƙa.

Labarai24 dai ba ta san asalin wannan barkwanci ba tsakanin mutanen biyu.

Daga lokaci zuwa lokaci, mutanen biyu sukan wallafa rubutu na tsokana a shafinsu na Facebook, inda mabiyansu suke bayyana ra’ayoyinsu cikin raha.

A ranar Talata Labarai24 ta ci karo da wani rubutu da Zango ya wallafa, inda ta tattaro muku kaɗan daga cikin irin tsokacin da mabiyansu suka yi.

Tun da farko Zango ya rubuta:
“Dole ne a sara wa mata ko mutum ya gane kurensa. Allah ya ƙaro danƙon ƙauna da nauyin kafaɗa, CSP Magaji Musa Majia, Sardaunan Bompai, Ɗan Makwayon Sharaɗa, Babban Shamakin Nasir Zango”.

Wallafa wannan rubutu ke da wuya sai mabiyan Zango suka fara bayyana ra’ayoyinsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan