Jarrabawa Kyauta: Kwankwaso Ya Yi Alƙawarin Da Ba Zai Cika Ba

360

Wato ina ga Kwankwaso yana abin nan ne da Bature ke cewa ‘clever by half’. Ga wanda bai san me ake nufi da wannan azancin na Bature ba, sai ya nemi Magana Jarib Ce ta Ɗaya ya karanta labarin mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi (gumi). Kwankwaso ya yi hakan ne kawai don ya gaya wa mutane abin da suke so su ji ko da kuwa ba zai yiwu ba, musamman tun da ya lura mutane son ransu ne a gabansu ba son gaskiya ba.

Amma da mutane gaskiya suke so, da sai su tambaye shi, mun ji za ka bayar da wadannan kyauta ga ‘ya’yanmu, amma ya kamata ka gaya mana ta yaya? Manufarsa dai ya janyo hankalin iyaye da matasa, wanɗanda su ne kashi 70 na masu zaɓe, tun da kowa son na bati yake yi Amma bari mu ga, shin hakan abu ne mai yiwuwa?

Da farko dai ina ganin an ma jahilci ya tsarin tarayya (federal) yake aiki a Najeriya. Tambayar farko ita, shin shugaban ƙasa na da wannan uko a tsarin mulkin Najeriya? Shin zai yiwu a tsarin gwamnatin tarayya ka iya hana biyan waɗannan kuɗaɗe a dukkan faɗin ƙasar nan?

Ko shakka babu, shugaban ƙasa na iya cewa a daina biyan waɗannan kuɗaɗen jarabawa, amma fa a matakin makarantun sakandire mallakin gwamnatin tarayya, wanɗanda yawan ɗalibansu bai wuce kashi 10 cikin 100 na yawan ɗaliban sakandiren Najeriya ba. Sauran kashi 90 ɗin dukkan su makarantu ne malllakin jihohi ne.

A jihar Kano misali akwai makarantun sakandire sama da 1000, amma guda huɗu ne kaɗai na gwamnatin tarayya— ta Unguwa Uku, ta Minjibir, ta Ƙaraye, sai ta Bukavu. Waɗannan makarantu kuwa yawan ɗalibansu bai kai kashi biyu na ɗaliban makarantun sakandire na Kano ba. To ina ga sauran kashi 98 na ɗaliban? Ya za a yi da su?

Rabi’u Musa Kwankwaso A Lokacin Da Ya Ƙaddamar Da Manufofinsa

Wata tambayar ita ce shin gwamnatin tarayya za ta hana Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare ta Afirka ta Yamma, WAEC, aiki a Najeriya ne? Ko kuwa gwamnatin tarayyar za ta riƙa biya wa ɗalibai kuɗin jarrabawar ne da na jiha da na tarayya?

Na faɗa a doka, shugaban kasa ba shi da iko a harkar ilmin jihohi. Wannan ne ya sanya baya ga hukumar kula da ilmin firamare ta gwamnatin tarayya, akwai hukumomin kula da ilimin firamare na jihohi, kuma kowane gwamna shi ke da ikon ya yi yadda yake so da kuɗaɗen hukumar a jiharsa. Don haka ba shi da ikon ya tursasa gwamnonin jihohi su biya wa yara kuɗin jarabawa kyauta.

Dandazon Jama’a A Taron Ƙaddamar Da Manufofin Kwankwaso

Na san wani zai ce to ai NECO da JAMB mallakin gwamnatin tarayya ne, don haka zai iya ba su umarni su ba da da fom kyauta ga ɗaliban jihohi. To a nan ma abin da kamar wuya. Domin dai, sai an koma zauren majalisa an tafka mahawara akan dokokin da suka kafa su, suka ba su damar su sayar da fom, wanda wannan abu ne da zai ɗauki lokaci.

Saboda dama tun da aka kafa hukumar JAMB ba aka ba ta dama ta sayar da fom, duk wanda ya zana jarabawar ba wanda ya taɓa yi y kyauta, shekara 30 da suka gabata. Ban ƙi ya ce zai rage mata kudi ba.

Su kuwa hukumomin NECO da WAEC, dama can gwamnatocin jiha ne suke biyan su kuɗaɗen jarrabawa, shi yasa ba a ganewa . Kuma ko da ɗin akan yi jarabawar mock (gwaji) idan ka ci a biya maka, idan ba ka ci ba ka sake. Sai dai daga baya abubuwa suka lalace aka ce, idan ba ka ci ba ka biya wa kanka.

Wata matsalar a dai akan maganar UTME da sauran su ita ce, samar da kuɗaɗen da za a yi hakan. Domin a wannan lokaci da tattalin arziƙi ke cikin wani hali, zai yi wuya gwamantin tarayya ta iya kwasar kuɗi ta ta kashe wa jihohi. Haka kuma shi a matsayinsa na shugaban ƙasa, bai isa ya tursasa gwamnatocin jihohi su biya wa yara kuɗin jarabawa kyauta ba, domin tsarin mulki bai ba shi wannan damar ba.

Hanya ɗaya da hakan za ta iya yiwuwa shi ne, ya nemi majalisun tarayya da na jihohi su yi wa kundin tsarin ƙasar nan gyaran fuska, a ɗauke ilmi daga jerin dokokin haɗaka, wato ‘concurrent list’, ya koma na gwamnatin tarayya kaɗai, wato ‘exclusive list’. Hakan kuma abu ne mai wuya.

Ni dai a gani na, wannan salo ne na bugun kura da gwado. A fake da guzuma don a harbi karsana.

Fatuhu Mustapha

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan