Shugaba Buhari zai buɗe aikin haƙo man fetur a Bauchi da Gombe

193

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da aikin tono man fetur a jihohin Bauchi da Gombe.

An dai gano tarin arzikin man fetur a jihohin biyu shekaru biyu da suka gabata

Jaridar Daily Trust ta ambato ƙaramin ministan man fetur na ƙasar Timipre Sylva, na cewa ”Za a gudanar da bikin fara tono man ranar Talata 22 ga watan Nuwamba Inda shugaba Buhari tare da wasu daga cikin ministocinsa za su halarta”

A shekarar 2016 ne kamfanin mai na ƙasar NNPC ya ƙaddamar da aikin binciko man fetur a arewacin ƙasar, abin da ya kai ga gano ɗimbim albarkatun man fetur ɗin a jihohin Bauchi da Gombe da Borno da kuma jihar Niger

A yayin da ƙasar ke dogara da man da ake tonowa daga yankin Niger Delta, Wannan shi ne karo na farko da za a fara tono man a yankin arewacin ƙasar, bayan da rikicin Boko Haram ya hana yunƙurin tono man a jihar Borno

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan