2023: Tinubu Ya Samar Da Manhaja Don Neman Taro Da Sisi Daga ‘Yan Najeriya

136

Kwamitin Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC zai ƙaddamar da wata manhajar da ya ƙirƙiro don neman taro da sisi daga ‘yan Najeriya.

Kwamitin ya ce ya kirkiro manhajar mai suna ‘Crowdfund’ don tara kuɗaɗen da zai yi amfani da su wajen gudanar da yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu.

Ta cikin manhajar ta Crowdfun, ‘yan Najeriya za su iya miƙa gudunmawarsu don mara wa takarar Tinubu baya.

Kwamitin ya ce manhajar za ta taimaka wajen taƙaita mu’amala da tsabar kudi a zaɓen 2023, kamar yadda majiyar Labarai24 ta rawaito.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan