Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi wa tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Aliyu Magatakarda Wamakko, ta’aziya, bisa rasuwar matarsa.
Shugaba Buhari ya bayyana saƙon ta’aziyyarsa ne a cikin wani saƙo da Mai Magana da Yawunsa, Garba Shehu, ya sanya wa hannu.
A cewar Shugaba Buhari, labarin rasuwar mai ɗakin Wamakko ya kaɗa masa zuciya.
“Rashin matar da ta kasance wani muhimmin ɓangare a rayuwark, uwar ‘ya’yanka, raɗaɗi ne mai wahalar riƙewa”, in ji sanarwar.’
Turawa Abokai