Gwamnatin Najeriya Ta Haramta Koyar Da Turanci A Makarantun Firamare

199

A ranar Laraba ne Gwamnatin Tarayya ta shigo da wata sabuwar manufa mai suna Manufar Harshe ta Ƙasa, NLP.

Manufar ta NLP ta mayar da koyar da harshen uwa dole tun daga aji 1 na firamare har zuwa aji 6.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana haka bayan kammala taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, FEC.

Adamu ya ce daga yanzu za a dinga amfani da harshen uwa a shekara shidan farko na firamare, yayin da za a fara koya wa ɗalibai Turanci daga Aji 1 Na Ƙaramar Sakandire.

Sai dai gwamnatin ta ce tana sane cewa aiwatar da wannan manufa zai yi wahala.

“Saboda haka, kodayake manufar ta fara aiki, Gwamnatin Tarayya za ta samar da kayan aiki da ƙwararun malamai da za su aiwatar da ita”, in ji Adamu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan