Indonesiya Ta Kafa Wata Sabuwar Doka Akan Mazinata

262

‘Yan majalisa a Indonesiya, sun amince da sabuwar dokar da ta haramta jima’i kafin aure a ƙasar.

A yanzu haka dai babban laifi ne a samu mutane sun yi zina, inda dokar ta ce duk wanda aka samu da laifin zai iya fuskantar zaman gidan yari da shekara guda, kamar yadda majiyar Labarai24 ta rawaito.

Dokar dai ta shafi ‘yan ƙasa da baƙi na ƙasashen waje kamar ‘yan yawon buɗe ido, a cewar BBC Hausa.

Haka kuma dokar ta hana daduro.

Dokar ta bai wa iyaye ko ma’aurata damar kai rahoto idan ɗansu ya aikata laifin, ko mata ko miji domin a yi musu hukunci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan