Pre – Wedding Picture: Kowanne tsuntsu…..

  4821

  Idan ka ga mummunan pre-wedding picture, irin ka ga amarya da angon na daƙuwa, ko ka ga sun rungumi juna, ko ka ga ya damƙo ƙugunta, ko an yi sumba, to alama ce da ta ke nuna cewa iyayen banza ne su ka raini ma’auratan, ko kuma ma’auratan sun bijirewa tarbiyyar da a ka ba su ne, ko kuma dama can sun saba damƙar juna tun kafin auren.

  Hakana in ka ga ballagazar amarya ta na ta cashewa a wajen bikinta, ko ka ga mazarin ango ya na ta botsare-botsare cikin rawa da sunan murna, to dukansu ba su da tarbiyya, kuma su ɗin, hoto ne mai magana na irin gurɓatattun ƴaƴan da za su zazzago duniya ne. Sun cuci ƴaƴansu, kuma sun cuci al’umma da suke shirin haifo baragurbi!

  Kwata-kwata babu cinyewa a fitsara lokacin biki. Angwaye da amaren da suka haifo manyan malamai da attajirai masu dattaku, tabbas ba su yi fitsara irin wannan ba. Sun ɓoye giggiwarsu da zumuɗinsu daga idon mutane saboda halin dattako, kawaici da tarbiyyar addini da a ka kwankwaɗa musu!

  Abin haushi, wannan al’ada ta rashin kunya ƙara samun gurin zama ta ke saboda manya sun baiwa yaran da ke Deejay jagorancin bukukuwa. Su Deejay ɗin fa ba malamai ba ne, ba masu karatu ba ne, ba manya ba ne! A a! Yara ne masu tara suma a ka kamar tsiko, ga wando saɓalikita, kuma fensir! To ta yaya mara kunya zai jagoranci bikin da Sunnar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ce ta zo da shi?

  Lallai ya kamata iyaye maza su karɓe ragamar sharholiyar aure daga hannun Iyaye mata. Domin, a yi haƙuri, da yawa mata ke shirya wa, kuma sai su miƙa gudanarwa a hannun Deejay da MC ɗinsa! Wai in ba a yi haka ba kamar ba a shaƙata ba! Ba komai! A ci gaba da shaƙatawa, daga baya kuma a yi ta haihuwar ƴaƴan banza!

  Mubarak Ibrahim Lawan ya rubuto daga Kano Najeriya

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan