Kannywood ta ƙara babban rashi

2534

Abdulwahab wanda aka fi sani da Awarwasa ya rasu ne ayau Litinin.

Matashin jarumin dai ya rasu ne bayan yayi fama da rashin lafiya.

Mujallar matashiya ta ruwaito cewa, Ɗan wasan Hausan ya rasu yayin da ake ci gaba da jimamin rasuwar Kamal Aboki wanda shima ya rasu sakamakon hatsarin mota akan hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Shi dai Awarwasa ɗan jihar Kano ne kuma ya fito a fina-finai da dama.

Daga cikin fina-finan da ya fi shahara, akwai; “A Duniya”, shirin mai dogon zango.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan