Kwankwaso Ya Fito Takara Ne Don Ya Ci Zaɓe Ba Don Ya Janye Wa Wani Abu Ba—- NNPP

73

Jam’iyyar NNPP ta ce ɗan takararta, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya fito takarar ne da nufin ya ci zaɓen 2023 ba ɓata lokaci ba.

Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen NNPP, Ladipo Johnson ne ya bayyana haka ranar Lahadi a Abuja.

Mista Johnson ya ce yana mayar da martani ne game da masu yaɗa farfaganda akan takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar.

“Tun da farko, sun fara yaɗa farfaganda game da cewa Kwankwaso zai janye wa ɗan takararsu mara ƙwari”, in ji Mista Johnson.

A cewarsa, masu irin wannan farfaganda sun kasa siyar da ɗan takararsu ne ga ‘yan Najeriya.

“Waɗannan ‘yan siyasa suna yunƙurin tallata ɗan takararsu ta hanyar amfani da kuɗi don siye ‘yan NNPP ko ‘yan Kwankwasiyya”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan