Masu sana’ar ‘Faci’ a Najeriya sun yi ƙarin kuɗi

1593

A Najeriya ƙungiyar masu sana’ar Faci wato Vulcanizers Association of Nigeria reshen ƙaramar hukumar Karu da ke jihar Nasarawa sun yi shelar karin farashi kan abin da suka kira karin haraji da hauhawar farashin kayayyakin da ake amfani da su don gudanar da wannan sana’ar.

Shugaban kungiyar na ƙaramar hukumar ta Karu Mista Adegwai Antony ne ya sanar da haka a yau Litinin a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema Labarai.

Mista Antony ya ce sakamakon hauhawar farashin kayayyakin da su ke amfani da su a wannan sana’a da kuma haraji da su ke fuskanta daga gwamnati ya sanya su ɗaukar matakin wanda ya fara daga yau Litinin.

Haka shugaban masu facin ya shaidawa Labarai24 cewa nan gaba kaɗan za su zauna da uwar kungiyar masu faci reshen jihar Nasarawa domin ganin wannan karin farashi ya game Najeriya gaba ɗaya.

A sabon farashin dai za a caji masu kekunan da aka yiwa Faci Naira Dari Uku (₦300) inda za a caji masu babur kuma za su biya Naira Dari Biyu (₦200).

Ga dai jadawalin farashin kamar haka:

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan