CBN Ya Magantu Game Da Wa’adin Daina Karɓar Tsaffin Kuɗi

10528

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, ya ce ba zai ƙara wa’adin daina karɓar tsaffin kuɗi na 31 ga Janairu ba.

Mista Emefiele ya bayyana haka ne ranar Talata a Abuja a yayin taron tattaunawa na Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗi, MPC, na babban bankin.

A cewarsa, kwana 90 da CBN ya ba ‘yan Najeriya don su kai tsaffin kuɗinsu bankuna ya isa.

“Mun yi kira ga bankuna da su ƙara sa’o’in da suke aiki kuma su yi aiki har a ƙarshen mako.

“Ba dalilin da za a ce a ƙara lokaci. Akwai sabbin kuɗin nan sosai “, in ji shi.

Dama dai kiraye-kiraye sun yawaita ga CBN cewa ya ƙara wa’adin daina karɓar tsaffin kuɗin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan