Iyayen Wata Budurwa A Neja Sun Ƙi Karɓar Sadakin ‘Yarsu Da Aka Biya Da Tsaffin Kuɗi

1214

Iyayen wata budurwa a ƙaramar hukumar Gbako dake jihar Neja sun ƙi karɓar sadakin da saurayin ‘yarsu ya bayar da tsaffin kuɗi.

Jaridar City & Crime ta rawaito cewa saurayin budurwar ya kai kuɗi gidan su budewar tasa da suka haɗa da na sadaki da na sauran shirye-shirye.

Ba a dai ɗaga bikin ba, amma iyayen budurwar sun lura cewa saboda wa’adin da Babban Bankin Najeriya, CBN, ya sa na daina karɓar tsaffin kuɗi ba za su iya yin dukkan siyayyar da suke so ba, kuma ba su da asusun banki.

Wani ɗan uwan saurayin budurwar ya ce: “Mun kai kuɗi gidan su budewar da za mu aura. Ranar Lahadi suka kira ni cewa in zo in karɓi tsaffin kuɗin har sai mun samu sabbi. Suka ce ba su san ina za su je su sauya tsaffin kuɗin ba. Ina so mu mayar da su banki har zuwa lokacin da za mu samu sabbi”, in ji shi.

Tuni dai wasu suka daina karɓar tsaffin kuɗi a ƙasar nan tun ma kafin wa’adin da CBN ya sa ya cika.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan