Kabiru Sufi ya zama Dan Adalan masarautar Dambatta

1603

Sarkin Fulanin Dambatta da ke jihar Kano, Alhaji Aminu Bello Sulaiman ya amince da naɗin Dr. Kabiru Sa’id Sufi a matsayin Dan Adalan ƙasar Dambatta.

Sanarwar naɗin na ƙunshe cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Fulanin Dambatta ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin shirye – shirye Dr. Bello Adamu Namura.

Dan Adalan Dambatta, Dr. Kabiru Sa’id Sufi

Sanarwar ta ce “Bisa dogon nazarin halayenka da kuma la’akari da gudummawarka ga Dambatta, jihar Kano da kasa baki daya, da kuma girmama masarautar Dambatta, Mai girma Sarkin Fulani-Dambatta ya umarci a sanar dakai cewa kana daya gada cikin wadanda ya amince a baka mukamin sarautar DAN ADALA a kasar Dambatta

Sanarwar Da Sarkin Fulanin Dambatta ya aikewa da Dr. Kabiru Sa’id Sufi

Saboda haka an tsara jadawalin shirye shirye da tsare tsaren bikin nadin, wanda da zajar an gama shirye shiryen bikin nadin sarautar, kwamitin tsare tsaren zasu sanar da kat lokacin da za’ayi bikin nadin da zarar an sa rana”

“A madadin Mai girma Sarkin Fulani, muna tayaka murnar samun warnan sarauta da kuma addu’ar Allah Ya tayaka riko, Ya zama jagora bisa wannan amana da nauyi daya dora maka. Muna kuma fatan za’a bada hadin kai wajen bin umurni da dokokin wannan masarauta”

Dakta Kabiru Sufi babban malami ne a kwalejin share fagen shiga jami’a da ke jihar Kano, mamba ne a ƙungiyoyi da dama a ciki da wajen Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan