Fitacciyar jarumar barkwanci, Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso), ta yi tsokaci kan masu cewa ya kamata ta daina irin wannan wasan saboda shekarun ta.
Daso ta na daga cikin ‘yan wasan barkwanci da ke baje-kolin su sosai a dandalin soshiyal midiya a yanzu, inda ake ganin guntayen bidiyoyin ta a Instagram, TikTok, WhatsApp Status da YouTube.
Ta ce: “To ai wannan ba wani sabon abu ba ne. Da man can da wasan barkwanci aka san ni, don farko da shi na fara. Saboda haka ma bai kamata mutane su rinƙa magana a kai ba.”
Amma akwai wasu ‘yan kallo da ke cewa ya kamata shaharariyar jarumar ta kama girman ta yanzu a matsayin ta na dattijuwa, wai bai kamata ta ci gaba da taka irin wannan rol ɗin ba, kawai ta bar wa yara.
Ta yi ƙarin bayani da cewa, “Ai kayan mutum a san shi a kan aikin sa. Da kamar Hadizan Saima ce aka ga ta na yin hakan sai a yi magana saboda ba a san ta da irin wannan rol ɗin ba, amma duk duniya da haka aka san ni, don ko a kan hanya mu ka haɗu da mutane sai ce ai kamar ba ni ba saboda ba su gan ni ba kamar yadda yadda su ka saba gani na ba a fim.
“Don haka fitowa irin wannan yanzu aka fara, tunda abin ya bi jiki na, da haka aka san ni.”
Ita kuwa a hirar da ta yi da mujallar Fim, Daso ta ce in dai wasan barkwanci ne, to yanzu ma ta fara.