2023: Atiku Abubakar ya yi alƙawarin farfaɗo da harkar tsaro tare da buɗe iyakokin Najeriya

116

Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin tutar jam’iyyar hamayya ta PDP Alhaji Atiku Abubakar, yayi alƙawarin sake buɗe iyakokin ƙasar nan da gwamnati mai ci ta APC ta rufe tare da alkawarin farfaɗo da tsaro a sassan ƙasar nan.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin yaƙin neman zaɓen sa da jam’iyyar ta gudanar a babban filin wasa na Sani Abacha dake ƙofar mata a birnin Kano a yau Alhamis 9 ga Fabrairu, 2023.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su tabbatar sun zaɓi jam’iyyar PDP daga sama har ƙasa a baban zaɓe mai zuwa domin samar da kyakkyawan sauyin da zai canja akalar ƙasar.

Ta cikin jawabinsa Atiku ya aike ga tambaya zuwa ga ‘yan jihar Kano da cewa” ya ku jama’ar jihar Kano, idan aka yi muku tambaya kan cewa a mulkin APC wanne abu kuka samu, zaku iya cewa ansamu wani ci gaba na ku zo mugani?.

”Idan har ku na so a farfaɗo muku da ingantaccen tsaro da bunkasa ɓangaren aikin noma ko kuma a sake buɗe muku iyakokin ƙasar nan, to ina mai shawartarku da ku zaɓi jam’iyyar mu ta PDP a babban zaɓe mai zuwa don samar da ci gaba” a cewar Atiku.

Haka kuma Atiku ya jinjinawa al’ummar jihar Kano bisa yadda su ka yi dafifi wajen tarbarsa tare da yin iƙirarin zama ɗa ɗaya tilo da zai yi aiki wajen farfaɗo da tattalin arzikin jihar da ma fannin tsaro.

Kafin wancan jawabi ɗan takarar shugaban ƙasar ya jagoranci buɗe wata babbar makarantar haddar karatun Alƙur’ani, da zata ɗauki ɗalibai maza 250 da mata 250 wanda Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya gina a unguwar Gunduwawa dake ƙaramar Hukumar Gezawa.

Wazirin na Adamawa ya kuma jinjinawa Sanata Shekarau, bisa wannan babban aikin da zai taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da yaɗa ilimin addinin Musulunci a makarantar da aka sanyawa sunan kakan mahaifiyar Sanatan, Gwani Mammadu Dan Gunduwawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan