Tinubu Ya Ce Ba Zai Yi Wa Arewa Komai Ba Idan Ya Ci Zaɓe— Naja’atu Bala

118

Tsohuwar ‘yar jam’iyyar APC, Naja’atu Bala Mohammed, ta ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ba zai yi wa Arewacin Najeriya komai ba idan ya ci zaɓe.

Naja’atu ta bayyana haka ne a cikin wani gajeren bidiyo da Labarai24 ta ci karo da shi.

“A taƙaice dai Tinubu ya yi min waya, ya gayyace ni washegari, da daddare ya yi min waya, ya ce ga shi ga shi yana Ingila, ya ji an ce na ƙi karɓar muƙamin da ya ba ni na ce i. Saboda ba ka faɗa min abin da za ka yi wa Arewa ba.

“Sai ya ce min yana Ingila. Ya siyo min tikiti in zo na ce masa a’a, ina da kuɗin tiket ɗina. Na ɗauki jirgi na biya kuɗin tiket ɗina, kashegari na je na same shi a Ingila, amma sun kama min otal, sun kama min otal, wannan magana ta gaskiya.

“To shi ke nan, da na je na zauna da shi, na isa Ingila kashegari da safe. Na je na zauna da shi, abin da na fara tambayar sa, da ya fara roƙona, don Allah don Annabi, Hajiya, haka ya dinga ce min. Wai in yi haƙuri don Allah”, in ji Najaatu.

“Ni kuma ba na so in yi izgili, in karɓi muƙamin da zai ban. Sai na ce ka daina haɗa ni da Allah. Amma me za ka yi mana a Arewa? Ya kalle ni tsabar idona ya ce babu abin da zan yi muku.

“Na ce kana nufin ba ka san halin da muke ciki a Arewa ba? Ga rashin tsaro? Ga ‘ya’yanmu suna ta gararamba? Almajirai? Ga tattalin arziƙinmu? Ga rufe boda,? Ga waye?

“Sai ya ce ya sani, amma in ina so ya saka, sai na ce kai yanzu, za ka yi takarar shugaban ƙasa amma ba ka da manufa da abin da za ka yi wa ƙasa?

“Sai ya ce min ba shi da shi. Abin da ya sa, zai dai yi kwandin manufofi. Abin da ya sa shi ba zai yi manufa ba, harkar tsaro wane ne ai kin ga sai a kashe ni”, ta ƙara da haka.

“Na ce wa zai kashe ka? Ai kin ga cewar idan na ce zan gyara soja, zan gyara ‘yan sanda, ai sai su kashe ni ma kafin lokacin.

“Saboda haka, ni in ba na ci zaɓe ba, ba zan yi wani tsari ma ƙasa ba. Haka ya ce min? Haka ya ce min. Ba ma zai yi wa ƙasar tsari ba”, in ji ta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan