Wasu fusatattun mata, a ƙarƙashin ƙungiyar ‘Angry Nigerian Women’ a yau Talata sun mamaye babban titin da ke kan hanyar zuwa babban ɗakin taro na ƙasa da ƙasa, wurin da ake tattara wa da sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, bisa zargin tafka maguɗi.
Jaridar Punch ta rawaito cewa matan sun kuma yi barazanar za su tafi tsirara idan har hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙi amincewa da bukatarsu kan dalilin da ya sa ba a aika sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ta hanyar yanar gizo zuwa babban ɗakin tattara sakamakon zaɓe na INEC yadda kowa zai gani.
Matan da ke rera waƙoƙi irin su ‘ba mu yarda ba’, ‘Mahmood ya nuna mana sakamako’, ‘asali sakamakon da muke so’ suma suna ɗauke da alluna ɗauke da rubuce-rubuce daban-daban da suka haɗa da, ‘INEC ki dena maguɗi’, ‘makomar ‘ya’yan mu muke ji, ‘Mahmood ka bamu sakamakonmu’, ‘mun gaji da zalunci’ da sauran su.