A yayin da ya rage ƙasa da kwanaki 5 Musulmai a faɗin Duniya su fara gudanar da ibadar Azumi, Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya buƙaci al’ummar musulmin Nijeriya da su fara duban jinjirin watan Ramadan daga ranar laraba mai zuwa.
Hakan na cikin wata sanarwa ce da sakataren mulki na majalisar ƙoli kan harkokin addinin musulunci na ƙasa, Zubairu Usman Ugwu ya sanyawa hannu.
Turawa Abokai