Asiya Balaraba Ganduje ta Kammala Digirin-Digirgir akan harkokin kasuwanci

147

Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje ƴar gidan gwamnan jihar Kano ta kammala digirin-digirgir, wanda a ka fi sani da PhD, ko Dakta, a makarantar koyar da harkokin kasuwan wato Paris School of Business (PSB) da ke kasar France.


A jiya ne Balaraba Ganduje, ta wallafa a shafinta na facebook, inda ta nuna godiya ga Allah bisa samun wannan nasara.


Asiya Balaraba Ganduje dai ta kammala digirin ne a fannin harkokin kasuwanci wato Business Administration.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan