Daga Ƙarshe Dai Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Ranar Fara Ƙidayar Jama’a

95

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za a fara ƙidayar jama’a da gidaje ranar 3 ga Mayu, 2023 a dukkan faɗin ƙasar nan.

Dokta Garba Abari, mamba a Kwamitin Wayar Da Kan Jama’a Game Da Ƙidayar Jama’a da Gidaje ne ya bayyana haka ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce za fara ƙidayar daga 3 ga Mayu, zuwa 5 ga Mayu, 2023.

A cewar Abari, aikin ƙidayar zai tattara bayanan kowane mutum, iyali da gine-gine.

Ya ce an samu sauyin ranar fara ƙidayar ne sakamakon ɗage zaɓen gwamnoni da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan