Kyaftin din kasar italiya, Leonardo bonucci ya sanar da cewa zai yi riyata a karshen kakar wasa mai zuwa.
Bonucci, ya na daya daga cikin manyan ‘yan wasan kwallon kafa a duniya, yayin da ya rage saura shekara daya kwantaraginsa ya kare da kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Mai tsaron bayan ya cika 36 da haihuwa a duniya.
Kamar yadda dan wasan ya fada cewa ‘’idan na daina buga wasa shekara mai zuwa, karshen tsaron baya yazo- yadda Italiya ke tsaron bayanta,’’.
Dan wasan ya fadi hakan ne a YouTube channel na kungiyar Juventus.
Bonucci ya na daya daga cikin wanda suka daukarwa Italiya kofin gasar Turai ta shekarar 2020, ya bugawa Italiya wasa 120, ya ci kofin Serie A sau 9- 8 a Juventus, 1 a AC Milan.
Dan wasan ya buga wasa na 500 a wasan da kungiyarsa ta Juventus ta fafata da Sevella a gasar Europa League a satin da ya gabata.