Gwamnatin Buhari ta amince da jinginar da filayen jirgin sama na Kano da Abuja

105

Gwamnatin Najeriya ta amince a jinginar da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma Mallam Aminu Kano da ke Kano.

Gwamnati ta amince da wannan mataki ne a taron majalisar koli da aka gudanar jiya a Abuja.

Ministan sufirin jiragen sama a Najeriya, Hadi Sirika, ya shaidawa BBC cewa za a jinginar da filin jirgin Abuja na shekara 20, sannan na Kano na tsawon shekara 30.

Sirika ya ce taron nasu ya kuma amince a sauyawa ma’aikatarsu suna daga ma’aikatar kula da sufirin jiragen sama zuwa ma’aikatar kula da sufirin jiragen sama da sararrin samaniya.

Ya kuma ce taron ya amince da wasu tsare-tsare da za su inganta harkokin sufirin jirage a Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan