Harkar Yaɗa Labarai: Kamfanin Trust Africa Media sun buɗe ofis a Kano

124

Kamfanin Trust Africa Media da ke gudanar da ayyukan da su ka shafi harkokin sadarwa, bayar da horo da kuma ɗab’i sun buɗe sabon ofishinsu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Shugaban Kamfanin na Trust Africa Media shiyyar Kano Mr. Tajuddeen Abdulrahman ne ya bayyana haka a jiya Laraba a hotel ɗin Tahir a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai.

Tajuddeen Abdulrahman ya ce sun buɗe ofishin na su ne a Kano la’akari da yadda jihar ta ke da miliyoyin al’umma kuma ta kasance cibiyar hada – hadar kasuwanci da siyasa a Najeriya.

Ya ƙara da cewa ayyukan da kamfanin na su ya ke yi sun haɗa da gudanar da aikin jarida a shafukan intanet da tallace-tallace da buga kalandu da littattafai ga masu bukata da kuma bayar da horo na musamman akan kafafen sadarwa na zamani.

Ya ƙara da cewa Kamfanin na Trust Africa Media yana gudanar da aikin fassara daga harshen turanci zuwa harshen Hausa ko kuma mayar da rubutun Hausa zuwa harshen Turanci da kuma kula da shafukan sadarwa na fitattun mutane da su ka haɗa da ƴan siyasa da kuma ƴan kasuwa.

Tajuddeen Abdulrahman ya ce nan gaba kadan za su ƙaddamar da jaridarsu wacce za ta dinga kawo labarai cikin harshen Hausa da Turanci wanda su ka shafi jihar Kano kai tsaye.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan