Shekararsa uku kawai da zama mai horarwa – kamar ɗalibine a “Level 300” na jami’a. Babban ɗan wasansa shine Bukayo Saka – wani ɗan yaro ɗan shekaru 21 da ya fara farawa a Arsenal shekaru biyu da suka wuce. Kyaftinsa wani matashin yaro ne Odegaard – gaba ɗaya shekarunsa 24 kuma yazo ƙungiyar shekarar da ta wuce. Mai ci masa ƙwallo wani yaro ne Martinelli ɗan shekaru 21 wanda wannan itace kakarsa ta farko a matsayin mai fara buga wasa. Mai tsare masa baya wani yaro ne ɗan shekaru 20 William Saliba da bai taɓa buga firimiyar Ingila ba sai bana. Wanda yafi kowa ƙwarewa a ƙungiyarsa wani ƙaramin ɗan wasane Granit Xhaka wanda bai taɓa cin wani kofi mai tarihi ba a rayuwarsa. Sai Thomas Partey mai yawan jin rauni. Sai Jesus safaya taya wanda ya dawo daga dogon rauni. Da sauransu!
Abinda Mikel Arteta yayi a kakar bana abu ne da aka daɗe ba’a yi ba. Sai dai masu ƙarancin fahimtar ƙwallon ƙafa ba zasu gane ba. A Italiya maki 81 ke bada Serie A, a Andalus maki 82 ke bada Laliga, a Faransa maki 80 ne ke bada Ligue 1. Mikel Arteta ya ja tawagar yara sun ci maki 81 a sati na 36 a firimiyar Ingila, duk da cewa akwai ƙungiyoyi guda huɗu da suka fishi zaƙaƙuran ƴan wasa, amma masu fashin baƙi sun ce ya kasa, bai iya ba, bashi da ƙwarewa.
Sun manta cewa abokan hamayyarsa tsohon megidansa ne Pep Guardiola – kocin da ba’a taɓa kamar sa ba a tarihi – wanda ya fara koyarwa shekaru 15 da suka wuce. Da Jurgen Klopp, shahararren mai horarwar nan na Liverpool da ya fara horarwa shekaru 20 da suka wuce. Da Erik Ten Haag, kocin Manchester United daya fara horarwa shekara 13 da suka wuce. Da Eddi Howe, kocin Newcastle daya fara horarwa shekaru 10 da suka wuce. A tsakaninsu, Arteta kamar ɗalibin jami’ane a bainar farfesoshi, wanda kuma ya taka rawar da ta kere tasu.
Masu sharhi na cewa ai Liverpool ma sunyi ƙoƙari a baya, wanda gaskiya ne. Sai dai bambancin Arsenal da Liverpool shine kocin Arsenal yaro ne, na Liverpool kuma tsohon hannune. Har yanzu Arsenal bata da kamar Salah, Mane, Firmino, Wijnaldum, Fabinho, Arnold, Robertson, Allison da Van Dijk. Amma duk da haka ta zamo ƙungiya ta farko data nuna Manchester City da yatsa. Har yanzu Arsenal bata da mashahurin ɗan wasa kamar Harry Kane, De Bruyne, Casemiro, Haaland, Bruno Fernandez, Riyadh Mahrez ko Marcus Rashford. Amma duk da haka gogayya take da manyan ƙwari. Ba kuma kowa ne sanadi ba face Mikel Arteta.
Me yiwuwa bugun hatsin da Manchester City ɗin ta yiwa Real Madrid a daren yau yaja hankalin masu sharhi, su lura cewa yaƙin da Arsenal tayi a wannan kakar ba ƙarami bane.
Wanda ya rubuta: MA Iliasu