Na yi nadamar goyon-bayan Tambuwal a lokacin da ya zama shugaban majalisa -Gbajabiamila

74

Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce ya yi nadamar jagorancin tafiyar da ta bai wa Aminu Tambuwal nasarar zama kakakin majalisa ta bakwai a Najeriya.

Gbajabiamila ya shaida wannan nadamar tasa a lokacin da ya ke tsokaci kan ‘yan majalisar baya da ya taimakawa bayan adawa da zaɓin jam’iyya.

Shugaban majalisar ta wakilai, na wadannan kalamai ne a wani zaman haɗin-gwiwa tsakanin sabbin ‘yan majalisa na APC da kuma sauran jam’iyyun adawa da ke shirin shiga majalisa ta 10 da zaran an kaddamar da ita.

Gamayar ta amince da zaɓin da jam’iyyar APC tayi na Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu a matsayin shugaba da mataimakin majalisa ta 10.

Har yanzu ana cigaba da gudanar da wannan zama a Transcorp Hilton, da ke Abuja

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan